
IDAN GASKIYA TA BAYYANA MU DAGE MU YADATA GA AL’UMMA, KADA MU BOYE DON KAR MU BAIWA MAI WANNAN GASKIYAR CREDIT DINSHI, SABODA BAMA SONSHI…….Masu hikima sunce zaka iya rayuwa a cikin gawurtaccen gida wanda ba’a rasa komai a cikin gidan ba. Amma ka kasance a cikin kunci da damuwa. wani kuma yana a cikin kauye a kauyenma a cikin bukka amma yafi mai wadata jin dadi da farin ciki da rayuwa mai dadi. Jim dadin aure a zuciya take ba’a kyakyawan gida, kyawawan tufafi, tarin dukiya, kayan alatu ko kyan mace ko kyawun na miji ba. Soyayya babu dalili itace soyayya, ba soyayya mai dalili ba.godiya ga Allah ba ba yin sallah ko azumi ko zuwa ummara ne ba. Kyautatawa iyali da arzikin da Allah S.W.T ya baka da kyautatawa Al’umma shine godiya ga Allah. Mu zama masu yabawa juna idan akayi abin yabawa ko fadawa juna kuskurensu idan akayi kuskure. MU AJIYE SON ZUCIYA, HASSADA, BAKIN CIKI, KYASHI, TSANA BABU DALILI, ITACE KADAI KOFAR BULLEWA A WURIN MUSULMIN AREWACIN NIGERIA.
Mene Ra’ayinku akan wanan kalaman?
