DA DUMI-DUMI: Ƴan Zanga-Zanga Sun Ƙona Bankin Access a Delta
Rahotanni da ke shigo mana na nuni da cewa Masu zanga-zanga sun bankawa bankin Access wuta da kadarorin bankin a Udu dake Warri jihar Delta
Zanga-zangar adawa da Karancin kudin sabbin Naira ya fara ne a kan titunan Udu kafin ta rikide zuwa tashin hankali, wanda ya yi sanadin kona gine-gine da dukiyoyi a Jihar.
